Daily Post Nigeria Ku samar da kaya masu inganci ko ku rasa lasisin ku – SON Home News Politics Metro Entertainment Sport Hausa Ku samar da kaya masu inganci ko ku rasa lasisin ku – SON Published on December 19, 2024 By Hafsat Bello Hukumar kula da ingancin kayayyaki ta kasa SON ta yi kira ga masana’antu da su tabbatar da cewa kayayyakin da suke samarwa suna bin ka’idojin Ma’auni na Masana’antu na Najeriya (NIS), ko kuma su fuskanci rasa lasisin su. Shugaban Hukumar SON, Dakta Ifeanyi Chukwunonso Okeke, ya yi wannan kiran yayin bikin bayar da takardun shaidar cika ka’ida ga kamfanoni 52 da suka cika ka’idojin MANCAP a Kano. Da yake wakiltar shugaban, Ko’odinetan Hukumar a Kano Office II, Dakta Ado Ibrahim, ya ce, “Takardar shaidar MANCAP ba kawai wata alama ce ta karramawa ba, amma tabbaci ne ga masu amfani da kayayyakin cewa an gudanar da gwaje-gwaje sosai a kansu don tabbatar da ingancinsu.
” Shi ma da yake magana, Ko’odinetan Hukumar Kano Office I, Roger John, ya gargadi kamfanonin da suka samu takardun shaida da su ci gaba da bin ka’idojin, ko kuma su fuskanci barazanar rasa takardun shaidarsu. Related Topics: Don't Miss Wike ya kwace mallakin filayen Buhari, Abbas, Akume da wasu fitattun mutane 759 You may like Advertise About Us Contact Us Privacy-Policy Terms Copyright © Daily Post Media Ltd.
Top
Ku samar da kaya masu inganci ko ku rasa lasisin ku – SON
Hukumar kula da ingancin kayayyaki ta kasa SON ta yi kira ga masana’antu da su tabbatar da cewa kayayyakin da suke samarwa suna bin ka’idojin Ma’auni na Masana’antu na Najeriya (NIS), ko kuma su fuskanci rasa lasisin su. Shugaban Hukumar SON, Dakta Ifeanyi Chukwunonso Okeke, ya yi wannan kiran yayin bikin bayar da takardun shaidar [...]Ku samar da kaya masu inganci ko ku rasa lasisin ku – SON